Yanzu-yanzu: Shugba Buhari ya isa garin Zaria

Yanzu-yanzu: Shugba Buhari ya isa garin Zaria

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa garin Zaria da ke Jihar Kaduna a safiyar yau Alhamis 22 ga watan Augustan 2019.

Shugaban kasar ya kai ziyarar ne sakamakon gayyatan sa da Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya yi domin kaddamar da aikin ruwa garin Zaria da wasu muhimman aiki.

Baya ga aikin ruwan garin na Zaria, Shugaba Muhammadu Buhari zai kuma kaddamar da katafaren ginin babban bankin kasa CBN da aka yi wa lakabi da 'Centre of Execellence' duk a garin na Zaria.

Aikin ruwan Zaria yana daya daga cikin matsalolin da suka dade suna ciwa al'ummar garin tuwo a kwarya duk da cewa gwamnatocin da suka gabata sun yi ta alkawurran cewa za su magance lamarin amma abin bai kammalu ba sai yanzu.

Yanzu-yanzu: Shugba Buhari ya isa garin Zaria
Yanzu-yanzu: Shugba Buhari ya isa garin Zaria
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Ganduje vs Abba Gida-Gida: Kotu ta bayar da umurnin kamo wadanda suka kaiwa shaidan INEC hari

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel