Bashin miliyan N537.3: Kotu ta sahale wa AMCON ta kwace katafaren gidan tsohon gwamnan PDP

Bashin miliyan N537.3: Kotu ta sahale wa AMCON ta kwace katafaren gidan tsohon gwamnan PDP

Wata kotun tarayya da ke zamanta a jihar Legas ta umarci hukumar kula kadarori ta Najeriya (AMCON) da bankin UBA su karbi iko da gidan tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Donal Duke, da ke unguwar Ikoyi a jihar a garin Legas, bisa zargin ana binsa bashin N537,334,360.77.

Alkalin otun, Chuka Obiozor, ya bayar da wannan umarni ne bayan ya karbi wata takardar korafi mai lamba FC/L/SC/1373/2019 da AMCON da UBA suka gabatar a gabansa.

Daga cikin wadanda aka shigar da kara bayan Duke akwai kamfanin 'Stonehedge Investment Limited' da Owanari Bob-Manuel Duke.

Tun a ranar 8 ga watan Agusta Mista Obiozor ya zartar da wannan hukunci amma sai ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, kafafen yada labarai suka samu takardar hukuncin kotun.

Masu kara sun roki kotun ta basu izinin mallaka tare da rike gidan mai lamba 3 a kan titin Temple a unguwar Ikoyi, jihar Legas, a matsayin mallakinsu.

Sun sanar da kotun cewa Mista Duke ya saka hannu a kan yarjejeniyar cewa zai bayar da gidan gare su a lokacin da ya tsaya wa kamfanin 'Stonehedge Investment Limited' yayin da zai karbi aron kudi daga gare su.

DUBA WANNAN: Ta fara bayyana: Dalilin da yasa EFCC ke binciken tsohon gwamna Ambode

Alkalin kotun ya amince da bukatar masu kara tare da dakatar da tsohon gwamna Duke daga shiga ko yin kokarin kara gudanar da wata hulda da ta shafi ya yi amfani ko bayyana gidan a matsayin mallakinsa.

Alkalin ya umarci AMCON da UBA a kan su bawa wanda ake kara wa'adin kwanaki 20 domin ya biya bashin kudin ko kuma kotu ta mallaka musu gidansa har ibada.

Bayan ya zartar da wannan hukunci, alkalin kotun ya daga zama a kan shari'ar har zuwa ranar 2 ga watan Satumba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel