Kwatsam: Najeriya ta rufe iyakar ta da Kotono, ta ritsa da dubban 'yan kasuwa

Kwatsam: Najeriya ta rufe iyakar ta da Kotono, ta ritsa da dubban 'yan kasuwa

A ranar Laraba ne Najeriya ta rufe babbar iyakar ta da kasar Benin da ke Seme a jihar Legas ba tare da wata sanarwa ba, lamarin da ya ritsa da dubban mutane da ababen hawa da ke jigila kullum a tsakanin kasashen biyu.

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa an rufe iyakar ne a ranar Talata bayan an kama wasu manyan motoci makare da kwayar 'Tramol' a Legas ranar 16 ga watan Agusta.

Rufewar ta cigaba har zuwa safiyar ranar Laraba, lamarin da yasa 'yan Najeriya yin dandazo a bakin iyakar bisa tsammanin za a barsu su dawo cikin kasar su.

Kazalika, rufe iyakar ya ritsa da 'yan kasuwar kasar Benin da ke son koma wa gida bayan da suka shigo Najeriya domin yin siyayya a kasuwannin garin Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda rufe iyakar ba tare da wata sanarwa ba ya shafa suna kumfar baki a dandalin sada zumunta ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Shugaban SPIP da Buhari ya umarci a bincika ya ki amsa gayyatar ICPC, ya garzaya kotu

Sunday James, kakakin rundunar hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), bai amsa sakon neman karin bayani da jaridar Premium Times ta aika masa ba. Amma hukumar hana fasa kwabri ta kasa (NCS) ta ce an rufe iyakar ne saboda wasu dalilan tsaro.

"Mu na gudanar da wani aiki na hadin gwuiwa da jami'an tsaron da ke aiki a iyakar Seme," kamar yadda kakakin hukumar Kwastam, Joseph Attah, ya tabbatar.

"Zai dauke mu kwamaki kafin mu kammala wannan aiki, kuma mu na iyakar bakin kokarin mu domin ganin aikin bai shafi matafiya ba," a cewarsa.

Sai dai, jami'in ya gaza yin karin bayani a kan ko an fitar da wata sanarwa kafin fara aikin da ya jawo aka rufe iyakar wanda yin hakan kan iya gurgunta harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika ta yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel