Ku nisanci kabilanci - Sheikh Isa Fantami ya gargadi ma'aikatan ma'aikatar Sadarwa

Ku nisanci kabilanci - Sheikh Isa Fantami ya gargadi ma'aikatan ma'aikatar Sadarwa

Sabon ministan sadarwa, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, a ranar Laraba ya yi kira da ma'aikatan ma'aikatar da su mayar da hankali kan gudanar da ayyukansu kuma su guji kabilanci.

Dakta Pantami ya yi wannan gargadi ne yayinda yake jawabi ga ma'aikatar lokacin ya garzaya ofishi bayan rantsar da shi domin fara aikin ba tare da bata lokaci ba.

Ya yi kira ga ma'aikatan su zama tsintsiya madaurinki daya domin cimma burin da ake yiwa ma'aikatar.

Hakazalika ya tabbatarwa ma'aikatun da ke karkashinsa cewa zai kula da jin dadinsu domin cimman manufarsu.

KU KARANTA: Hotunan bikin rantsar da ministoci da ya gudana a fadar shugaban kasa Abuja

A cewarsa: "Wannan aiki ba nawa kadai bane, wajibi ne mu hada kai matsayin yan'uwa domin cimma burinmu."

"Idan mukayi abinda ya dace, tarihi zai yi mana kyau. Amma idan muka yaudari al'ummarmu, tarihi zai yi muni garemu."

"Mun sani hakkin da ke kan dukkan ma'aikatun da ke karkashin ma'aikatar kuma mun san rawar da ya kamata ma'aikatar ta dauka."

Ministan ya ce akwai kalubale da dama a bangaren sadarwa amma shirye yake da dakilesu domin ciyar da bangaren gaba.

Ya ce za'a shirya wani taron kwanaki biyu domin tattaunawa da samar da mafita kan kalubalen da kuma yadda yake son gudanar da mulkinsa.

Sakataren din-din-din na ma'aikatar, Istifanus Fuktu, ya yi maraba da ministan kuma ya yi kira da shi ya mayar da hankali kan kalubalen da ma'aikatar ke fuskanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel