Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da Hamisu Wadume, kasurgumin mai garkuwa da mutane

Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da Hamisu Wadume, kasurgumin mai garkuwa da mutane

A ranar Litinin, 19 ga wtaan Agusta 2019, jami'an hukumar yan sanda karkashin jagorancin DCP Abba Kyari sun damke gawurtaccen ami garkuwa da mutane, Alhaji Hamisu Wadume.

An damkeshi a Layi Mai Allo Hotoro jihar Kano.

Da farko an damke Wadume ne a ranar Talata 6 ga Agusta amma wasu sojoji suka budewa yan sandan dake tafe da shi wuta inda suka kashe yan sanda 3 da masu farar hula 2. Sai Wadume ya sake guduwa.

Ga abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da shi:

1. Ainihin sunansa Hamisu Bala, ana masa inkiya da Wadume

2. Bahaushe ne wanda mahaifin kakansa yayi hijra daga jihar Katsina zuwa Taraba. An haifeshi da karamar hukumar Ibbi. Mahaifinsa, Bala, ya auri mahaifiyarsa daga kabilar Tibi na jihar Benuwe.

3. Wadume ya kammala karatunsa na sakandare inda ya halarci makarantar Government Secondary School (GSS) Ibi.

KU KARANTA: Hotunan gidan da aka damke Hamisu Wadume a Hotoro, jihar Kano

4. Wadume ya kasance dan kasuwan kifi, mai penti, dan siyasa kuma yana auren mata hudu.

5. A zaben 2019, Wadume ya tsaya takarar dan majalisar dokokin jihar Taraba mai wakiltan Ibbi karkashin jam'iyyar Young Democratic Party (YDP) amma bai samu nasara ba.

6.A shekaru biyu da suka gabata, Wadume yayi kudi lokaci daya inda ya ginawa abokansa gidaje kuma ya rabawa matasa motoci da babura. Kuma ya kasance mai kyauta ga jami'an tsaro.

7. An damke matansa biyu, sauran biyun kuma suna gudanar da aikin Hajji

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel