An daure wata mata tsawon shekaru 30 da laifin zubar da ciki, an wanketa bayan cin sarka ta shekaru 3 kacal

An daure wata mata tsawon shekaru 30 da laifin zubar da ciki, an wanketa bayan cin sarka ta shekaru 3 kacal

A ranar Litinin ne wata kotu a kasar Salvador, ta wanke wata mata da ake zargi da laifin kisa ta hanyar zubar da ciki, lamarin da ya ci gaba da gudana a kan harsunan mutane da dama a fadin duniya da kuma zaurukan sada zumunta.

Kasar Salvador dai ta yi kaurin suna a yayin da dokoki da muhukuntan shari'a na kasar ke daukar babban hukunci tare da bayyana fushi da murtuke fuska a kan mata masu zubar da ciki da gangan.

Matashiyar Evelyn Hernandez mai shekaru 21 a duniya, an daure ta na tsawon shekaru 30 a sakamakon laifin da ta aikata na zubar da ciki ta hanyar barar da dan tayin da ke cikinta, inda har ta ci sarka ta tsawon shekaru 30 a gidan dan Kande.

Kotun dai ya zuwa yanzu ta sallami Misis Hernandez wanda a baya aka samu da laifin kisa bayan tayi barin cikin jaririn da ta ke dauke da shi a watan Afrilu na shekarar 2016.

An yankewa Evelyn daurin cin sarka ta tsawon shekaru 30 tun tana mai shekaru goma sha tara a duniya, saboda tayi amfani da magunguna wajen barin cikin da ta dauka bayan wani yayi ma ta fyade.

Bincike ya tabbatar da cewa wani mutum ya yiwa Evelyn ta karfin tsiya wajen keta mata haddi tun a yayin da ta ke budurwa, lamarin da ya sanya ta dauki ciki ba tare da ta ankara ba har ya zuwa lokacin da ta kusa haihuwa, in da tayi amfani da magungunan zamani wajen barin jinjirin da ke cikinta babu rai.

KARANTA KUMA: APC ta yi martani kan simamen da EFCC ta kai gidan Ambode

A sanadiyar yadda kasar Salvador ta ke nuna bacin rai tare da murtuke fuska a kan zubar da ciki, an daure kimanin mata 147 har na tsawon shekaru 40 a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2014 kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Sai dai duk da tsattsauran ra'ayi na sabon shugaban kasar Nayib Bukele da ya mulki kusan watanni uku da suka gabata, ya nemi a sassauta dokar kasar ta hana zubar da ciki musamman idan ta shafi lafiyar uwar da ke dauke da cikin.

Da ta ke gabatar da jawabai ga dumbin al'umma masu taya ta son barka a gaban kotu, Evelyn cikin zubar hawaye ta yi wa Allah godiya tare da cewar akwai mata da dama da ke ci gaba da cin sarka a bisa kuskuren fahimta makamanciyar wadda ta kasance cikinta a baya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel