Ruwan sama ya yi sanadin mutuwar mutane 5 a cikin wasu gidaje 2 da suka rushe a Jigawa

Ruwan sama ya yi sanadin mutuwar mutane 5 a cikin wasu gidaje 2 da suka rushe a Jigawa

Akalla mytane 5 ne suka rigamu gidan gaskiya a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta yayin da wasu gidaje biyu suka rushe sakamakon mamakon ruwan sama da ya sauka kamar da bakin kwarya a jahar Jigawa.

Wannan lamari mai muni ya faru ne a wasu kauyuka guda biyu; Kuradage da Madachi dake cikin karamar hukumar Kirikasamma na jahar Jigawa, inda aka kwashe kwana da kwanaki ana ruwan sama wanda ya yi sanadiyyar rushewar gidaje da dama.

KU KARANTA: Gwamnan Ekiti ya umarci jami’an gwamnati su dinga magana da harshen Yarbanci

Shugaban karamar hukumar Kirikasamma, Alhaji Salisu Garba Kubayo ya bayyana cewa gidajen sun rushe ne yayin da ake tsaka da ruwan sama, inda mutane uku da suka hada da wata mata Halima Manu da yayanta biyu Aisha Manu da Dauda Manu suka mutu a kauyen Kuradage.

“Yayin da wani mutumi Musa Wuliwuli da matarsa Hauwa Musa suka mutu a kauyen Madachi. Bugu da kari ruwan ya rusa gidaje fiye da 200 a kauyen Kukadubu, gidaje 100 a kauyen Mattafari da kuma gidaje 30 a kauyen Kuradage.” Inji shi.

Shugaban karamar hukumar ya nemi gwamnatin jahar Jigawa da gwamnatin tarayya su kai ma mutanen da ambaliyan ruwan ya shafa dauki sakamakon ruwan ya mamaye fiye da kauyuka 30 a Kirikasamma.

Daga bangaren karamar hukumar, Salisu yace sun samar da dubunnan buhuhuna ga jama’an don tula musu kasa don su zama kariya ga gidaje.

A wani labarin kuma, ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake samu a daminar bana, musamman a watan Agusta ya lalata dubun dubatan gonakan manoma a jahar Jigawa, musamman a karamar hukumar Malammadori.

Lamarin ya faru ne a wasu kauyuka guda 9 dake karamar hukumar Malammadori, inda ruwan ya lalata akalla eka 12, 000 na gonakan jama’a. Daga cikin gonakan da ambaliyan ruwan ya shafa akwai na shinkafa, rogo, ridi da kuma dawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel