Aiki ga mai kare ka: Kasar Jamus ta koro 'yan Najeriya da suka ci zarafin Ekweremadu

Aiki ga mai kare ka: Kasar Jamus ta koro 'yan Najeriya da suka ci zarafin Ekweremadu

Hukumomi a kasar Jamus sun tiso keyar sahun farko na wasu 'yan Najeriya da ake kyautata zaton sune suka ci zarafin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, yayin da ya halarci wani taro da 'yan kabilar Igbo suka shirya ranar Asabar a kasar Jamus.

Wasu fusatattun mambobin kungiyar 'yan aware ta kabilar Igbo (IPOB) ne suka ci zarafin Ekweremadu yayin da ya halarci taron da aka gayyace shi a matsayin babban bako mai gabatar da jawabi.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen da kasar Jamus ta koro sun taso daga filin jirage na garin Frankfurt da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar Litinin kuma ana saka ran zasu sauka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas da misalin karfe 2:00 zuwa 3:00 na rana.

Babu tabbacin cewa iya wadanda suka ci mutuncin Ekweremadu kasar Jamus ta koro Najeriya. 'Yan sanda a kasar sun bayyana cewa sun kama wasu 'yan Najeriya a ranar da aka kai wa Ekweremadu hari.

DUBA WANNAN: Farfesa a jami'ar Najeriya ya yi murabus babu shiri bayan an fara tuhumarsa da yi wa daliba mai shekaru 16 ciki

Rex Osa, mai rajin kare hakkin 'yan gudun hijira, da ke zaune a birnin Stuttgart na kasar Jamus, ya shaida wa jaridar The Nation cewa, "jirgin sama dauke da wasu 'yan Najeriya ya tashi daga filin jirgi na Franfurt da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar Litinin kuma ana sa ran zai sauka a Najeriya da misalin karfe 2:00 zuwa 3:00 na rana.

"An kamo mutanen da ke cikin jirgin ne daga sassa daban-daban na kasar Jamus a tsakanin karfe 3:00 zuwa 5:00 na dare, sannan an tattara su a filin jirgi na Frankfurt domin a dawo da su Najeriya."

A cewarsa, "daga cikin mutanen da za a dawo da su Najeriya akwai marasa lafiya, a saboda haka mu na kira ga gwamnati da ta taimaka musu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel