Tabbatar da tsaro: Abubuwa 9 da ya kamata a kiyaye yayin tukin mota cikin ruwan sama - FRSC

Tabbatar da tsaro: Abubuwa 9 da ya kamata a kiyaye yayin tukin mota cikin ruwan sama - FRSC

Kamar yadda ya shahara a bakin masana, tukin mota cikin ruwan sama ya fi tuki da daddare hadari. A birnin tarayya Abuja da jihohin kusa irin Kaduna, an waye gari cikin ruwan sama kamar da bakin kwarya, kuma haka ma'aikata suka garzaya wajen aiki domin neman abinci.

Hakan ya sa hukumar kiyaye hadura a hanyoyin Najeriya FRSA ta bayyana abubuwabakwai da ya kamata mu sani yayin tukin cikin ruwa.

1. Kada kayi amfani da 'Cruise Control"

2. Ka rike tayar tuki (Steering) gam

3. Ka tabbatar share ruwar motarka (Wipers) na aiki da kyau

4. Ka tabbata tayar da na cike da iska

5. Ka tabbatar fa cewa birkin motarka ba tada matsala

6. Ka tsaya nesa da motar da ke gabanka

7. Ka kunna wutar gaban mota

8. Ka kiyayi hanyoyin da ruwa ya shanye

9. Idan ruwa ya shanye tayar motarka, kada ka juya tayar tuki (Steering), kuma kada ta taka birki

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel