Rikicin Hausawa da Yarbawa a Legas: Ainihin abinda ya faru - Hukumar yan sanda

Rikicin Hausawa da Yarbawa a Legas: Ainihin abinda ya faru - Hukumar yan sanda

Hukumar yan sandan jihar Legas ta damke mutane biyar tattare da rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Oke-Ado dake jihar Legas.

Jami'in hukumar, DSP Bala Elkana, ya bayyana ainihin abinda ya sabbaba wannan rikici da kuma matakin da jami'an yan sanda suka dauka domin kwantar da kuran kafin ya kai ga asarar rayuka.

Yace: " A ranar 18 ga Agusta misalin karfe 10 na safe, wani Alhaji Adekunle Habib na kasuwar Illepo ya kai kara ofishin yan sandan Oke Ode cewa an samu rashin jituwa tsakanin wani bahaushe da wani bayarabe dan tasha."

"Dan tashan na dauke da kaya a kansa sai Bahaushen turesa bisa kuskure inda kayan suka zube kasa. Kawai fada ya barke tsakaninsu biyu."

"Abokan matasan biyu suka shiga ma juna kawai sai samu yan baranda sukayi amfani da hakan wajen sace-sacen kayayyakin jama'a/

"Sun tare hanyar Legas zuwa Abekuta. Rikicin da ya fara tsakanin mutane biyu ya kusa zama rikicin kabila baicin zaburar hukumar yan sanda."

"Babu rayuwar da aka rasa, amma mutane hudu sun jikkata kuma suna jinya yanzu. An damke mutane biyar masu suna Kabiru Mohammed, Kabiru Adamu, Bashiru Mohammed, Saliu Madu, da Yusuf Amuda."

Elkana ya ce na kwantar da kuran kuma jami'ai na gudanar da sintiri domin tabbatar da tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel