Maganin mai yaudara: Kawaye uku sun hada kai sun yiwa saurayinsu dukan tsiya bayan sun gano yana soyayya dasu uku a boye

Maganin mai yaudara: Kawaye uku sun hada kai sun yiwa saurayinsu dukan tsiya bayan sun gano yana soyayya dasu uku a boye

- Wani saurayi dan kasar Kamaru ya yabawa aya zakinta, yayin da wasu 'yan mata da yake yiwa wasa da hankali suka gano shi

- 'Yan matan wadanda suke aminan juna sun gano cewa saurayin yana soyayya da duka su ukun a boye ba tare da sauran sun sani ba

- Dalilin da yasa 'yan matan suka shirya suka je suka same shi suka yi masa shegen duka suka tafi suka barshi a wajen

Wani mutumi dan kasar Kamaru ya gamu da gamonsa, bayan 'yan mata guda uku wadanda suke aminan juna sun yi masa dukan tsiya yayin da suka gano cewa yana wasa da hankalinsu wajen soyayya da su duka a boye.

Wannan dalilin ne yasa 'yan matan suka zauna suka shirya yadda za su kawo karshen lamarin, inda suka hada kai suka tunkari mutumin suka yi masa dukan tsiya, sannan suka gargadeshi akan kada ya kara shiga harkar su.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: Kwana biyu da daurin aurensu ango ya kashe kanshi bayan amaryarsa ta bayyana masa tana dauke da cikin wani kato

Wannan lamari da ya faru a kasar ta Kamaru ya jawo hankalin mutane da yawan gaske a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da Instagram, inda wasu ke ganin hukuncin da 'yan matan suka dauka bai kamata ba.

Wasu kuwa musamman mata da suka saba da irin wannan rainin wayo na samari sun bayyana cewa abinda 'yan matan suka yi daidai ne domin kuwa da yawa sun nuna idan sune a irin wannan halin irin wannan hukuncin zasu dauka.

Allah dai ya kyauta, ya kuma raba mu da yaudara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel