Gwamnatin Buhari ta fara aikin gina wani gada da zai hade Arewa maso Gabas da Abuja

Gwamnatin Buhari ta fara aikin gina wani gada da zai hade Arewa maso Gabas da Abuja

Injiniyoyi da kayan aiki sun fara isowa garin Ibbi da ke Jihar Taraba domin fara aikin ginin gada daga Ibbi zuwa zuwa Kogin Benue.

Zuwan Injiniyoyin da kayan ayyukan ya sa al'ummar garin murna duba da cewa sun kwashe kimanin shekaru 40 suna fafutikan neman a gina musu gadar.

Daya daga cikin mazauna garin, Alhaji Adamu Damper ya ce mutanen garin sunyi matukar farin cikin ganin injiniyoyi da wasu kayayakin aiki da suka iso garin domin fara aikin.

DUBA WANNAN: Wani matashi ya sheka barzahu bayan kashe dare da ya yi yana sukuwa da budurwarsa

Ya ce zuwan injiniyoyin da kayan aikin ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana mayar da hankali domin sharewa 'yan Najeriya hawaye kan abubuwan da suke bukata.

Alhaji Adamu ya ce mutanen Kudancin Taraba, Adamawa da wasu sassan Borno sun dade suna neman gwamnati ta gina musu wannan gadar tsawon shekaru 40 da suka gabata amma yanzu gwamnatin tarayya za ta fara aikin.

Alhaji Adamu, wanda tsohon shugaban karamar hukumar Ibbi ne ya yi bayanin cewa gadar za ta sada yankunnan Arewa maso Gabashin Kasar da Babban Birnin Tarayya Abuja idan an kammala ginin.

Kwamitin Zartarwa na Kasa ta ware zunzurutun kudi Naira Biliyan 70 domin aikin gadar a cikin kasafin kudin shekarar da ta gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel