Zamfara: Mutum 50 muke kashewa idan an kashe makiyayi daya - Shugaban 'Yan Bindiga

Zamfara: Mutum 50 muke kashewa idan an kashe makiyayi daya - Shugaban 'Yan Bindiga

Hassan Dantawaye shine kwamandan 'Yan bindiga da suka tuba a jihar Zamfara sakamakon sulhun da gwamnatin jihar tayi da su.

Shugaban 'Yan bindigan ya ce sun fara kai hare-hare da garkuwa da mutane da satar shanu saboda cin zarrafinsu da jami'an tsaro da 'Yan Sakai ke yi tare da rashin kulawa da matsalolin da suka fuskanta.

Dantawaye ya yi wannan jawabin ne cikin wata hira da ya yi da Maiharaji Altine inda ya tattauna kan batutuwa daban-daban da suka hada da dalilan da yasa suka fara kai hare-hare da kuma yadda sulhun da ake yi da su ke tafiya kawo yanzu.

Da aka masa tambaya kan kallubalen da ya ce makiyaya suna fuskanta daga bangaren jami'an tsaro da 'Yan Sakai, Dantawaye ya ce, "Jami'an tsaro musamman 'yan sanda suna cin zarafin mutanen mu, su kan karba kudade a hannun mu barkatai saboda gwamnati da al'umma suna mana kalon masu laifi.

DUBA WANNAN: Wani matashi ya sheka barzahu bayan kashe dare da ya yi yana sukuwa da budurwarsa

"Yan banga da 'Yan Sakai suma sun taka rawa wurin tabarbarewar lamarin saboda irin yadda suka cin mutuncin Fulani. Su kan kashe duk wani Fulani da su kayi tsamanin dan bindiga ne ko barawon shanu kuma gwamnati ba ta dauki wani mataki kwakwara a kai ba.

"Sun kashe mana mutanen mu da dama kuma da muka lura gwamnati ba za ta dauki mataki ba, sai muka fara daukan fansa, daga lokacin, muna kashe mutane 50 duk lokacin da aka kashe mana mutum daya."

Dantawaye ya ce ya fara garkuwa da mutane da kai hare-hare ne bayan ya rasa shanunsu kimanin 372 da tumakai masu yawa. Hakan ya sa shi da wasu makiyaya suka koma daji suka zama 'Yan bindiga domin ba su da wata mafita.

Sai dai a yanzu ya ce sun tuba sun rungumi sulhu saboda irin yunkurin da Gwamna Bello Matawalle ya yi na kare hakokinsu da kuma daukan alkawarin tallafa musu domin su koma rayuwa kamar yadda suka saba na kiwo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel