Jami’ar Wudil ta aika sunayen hazikan dalibai 296 ga Dangote domin ya basu aikin yi

Jami’ar Wudil ta aika sunayen hazikan dalibai 296 ga Dangote domin ya basu aikin yi

Jami’ar kimiyya da fasaha dake garin Wudil ta mika sunayen dalibai guda 296 zuwa ga kamfanin Dangote domin ta basu aikin yi, kamar yadda shugaban jami’ar, Aliko Dangote ya umarta.

Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Alhaji Musa ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace jami’ar ta tattara sunayen hazikan dalibai 296 daga tsangayoyin karatu daban daban.

KU KARANTA: Matashi ya hana gwamna shiga ofis saboda hakkokin mahaifinsa da aka danne

Farfesa Alhaji yace sun tattara daliban ne tun daga wadanda suka kammala jami’ar a shekarar 2012 zuwa yanzu, daga cikinsu akwai dalibai masu digiri mai daraja ta daya, watau First Class guda 16, yayin da guda 280 suke da digiri mai daraja ta 2, watau 2:1.

“Bisa cika umarnin shugaban jami’a Alhaji Aliko Dangote GCON, mun tattara sunayen dalibai 296 da suka kammala daga jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil daga tsangayoyi daban daban tun daga shekarar 2012 zuwa yanzu.

“Mun mika sunayen ga kamfanin Dangote domin basu aiki, daga cikinsu akwai dalibai 16 masu digiri mai daraja ta daya, yayin da 280 ke biye dasu da daraja ta biyu. Zamu cigaba da bin Kadin sunayen har sai an samu biyan bukata. Dalibaina za su cigaba da zama abin alfahari na.” Inji Farfesa Shehu Alhaji.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne Dangote ya yi alkawarin daukan zakakuran daliban jami’ar Wudil aikin yi, sa’annan ya yi alkawarin samar musu da ingantaccen wutar lantarki nan bada jimawa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel