Wani mai wa'azi ya sha da kyar hannun matasa bayan an gano barawo ne

Wani mai wa'azi ya sha da kyar hannun matasa bayan an gano barawo ne

Wani mai wa'azin addinin kirista mai shekara 49, Mista Akinjide Durojaiye ya sha kyar bayan an masa dukkan tsiya a wani shago da ya shiga domin yi musu wa'azi a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Mai wa'azin a cocin Dominion Assembly da ke Ilare-Ijesa na jihar Osun ya yi ikirarin cewa 'Allah' ne ya umurce shi ya tafi shagon masu sayar da wayoyin da ke ginin Femi Johnson Dugbe a Ibadan domin ya yi musu wa'azi.

Sai dai daga bisani an gano ya sace wayoyi biyu a shagon da kudinsu ya kai N70,000 inda ya boye a wani lungu amma kuma aka gano shi aka kwace wayoyin sannan aka nakada masa dukan tsiya.

DUBA WANNAN: Wasu boyayyun kananan kasashen duniya 6 da ba kowa ya san su ba

A yayin da ya ke amsa laifinsa, ya ce shaidan ne ya rinjaye shi ya yi satar domin ya sayar ya samu kudin yi wa yaron mai shekara 7 magani bayan ya fado daga wani gini mai bene 2.

Daga baya dai fusattatun mutanen sun sake shi bayan wasu sun sanya baki duba da cewa ya yi laushi sosai.

Mutanen sun ce sun san shi kuma ya shiga mawuyacin hali ne bayan matarsa ta nemi a raba aurensu ta bar shi da yaran da suka haifa ya ringa kulawa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel