Wasu boyayyun kananan kasashen duniya 6 da ba kowa ya san su ba

Wasu boyayyun kananan kasashen duniya 6 da ba kowa ya san su ba

Akwai kimanin kasashe fiye da 200 a duniya amma akwai wasu kasashen da mutane da dama ba su san da su ba. Wasu daga cikinsu ba su da girma kuma al'ummar da ke zaune a kasashen tsirarun iyalai ne kawai.

Ga jerin kasashe 7 masu karancin al'umma inda wasu ba su yawan mutanen da ke wani birni ko kauye ba.

1. Palau

Jamhuriyar Palau kasa ce zagaye da teku. Palau tana daya daga cikin wurare masu matukar ban sha'awa a duniya. Tana da fadin sakwaya kilomita 459 da yawan al'ummma da suka kai 21,347.

2. Niue

Niue karamar alkarya ce da ke Oceania. Sai dai duk da irin kyawun da kasar da ke shi masu yawon bude ido ba su cika zuwa kasar ba. Saboda haka kasar dogar ne daga tallafin da ta ke samu daga kasar New Zealand. Al'ummar da ke kasar ba su fi 600 ba.

DUBA WANNAN: Shahararrun 'yan wasa 15 da ba su taba buga wa kasarsu ta haihuwa kwallo ba

3. Saint Kitts and Nevis

Kasar da kunshi alkaryu biyu: Saint Kitts da Nevis. Daya daga cikin hanyoyin samun kudin shigarsu shine sayar da izinin zama dan kasar ta hanyar saka hannun jari a masana'antar sarrafa sugar na kasar ko kuma sayan kadara da ba ta gaza $400,00 ba.

4. Tuvalu

Tuvalu yana daya daga cikin kasashe mafi kankanta da kuma talauci a duniya. Talaucin da kasar ke fama da shi ya yi muna har ta kai ga cewa an ba ta addreshin intanet na .tv wadda hakan ya zama hanyar samun kudin shiga ga kasar.

5. Nauru

Nauru itace jamhuriya mafi kankanta a duniya. Kasar ba ta da babban birnin ko ingantaccen hanyayin zirga-zirga. Matsalolin yanayi da ake yawan samu a kasar yana hana masu yawon bude ido zuwa kasar. Kuma kashi 70 cikin 100 na mutanen kasar na fama da matsanancin kiba.

6. Jamhuriyar Molossia

Jamhuriyar Molossia karamar kasa ce da Kevin Baugh ya kafa a cikin Jihar Nevada na kasar Amurka. Mutanen da ke kasar sun hada da Mista Baugh da kansa, iyalansa, karnuka 3, mage 1 da zomo 1. Kasar na tutar ta da taken kasa har ma da fasfo din zama na kasar. A Mayun 2019 Jamhuriyar da cika shekaru 42 da kafuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel