Zuwa Indiya neman magani: Amurka na kulla wa Zakzaky makirci ta hannun FG - IMN

Zuwa Indiya neman magani: Amurka na kulla wa Zakzaky makirci ta hannun FG - IMN

Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) ta zargi Gwamnatin Tarayya da wasu jami'an kasar Amurka da yunkurin kawo cikas ga tafiya neman lafiya da shugabansu, Sheikh Ibrahim Zakzaky tafi a kasar India.

Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat sun tafi birnin New Delhi a India ne bayan belin da babban kotun jihar Kaduna ta ba su a ranar Litinin 12 ga watan Augusta domin su tafi a duba lafiyarsu.

Sai dai wata jawabi da Sakataren Kungiyar ta IMN, Abdullahi Muhammad Musa ya fitar a ranar Laraba, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Najeriya da wasu jami'an Amurka sun hana shugabansu ya ga likitoci kamar yadda kotu ta ba shi dama.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishinan 'Yan sanda ya fadi wadanda ke daukan nauyin 'yan bindiga a Najeriya

Musa ya yi ikirarin cewa jami'an gwamnatin Najeriya da suka yi wa shugabansu rakiya zuwa asibitin Madenta da ke New Delhi "sun ki barin likitocin da ya bukaci su daba shi da mai dakinsa duba su yadda ya kamata."

Ya kara da cewa ingantattun majiya ta tabbatarwa kungiyar cewa ofishin jakadancin Amurka da ke India ya umurci mahukunta asibitin kada su amince su karbi Zakzaky domin yi masa magani.

"Shiekh Zakzaky da kasan ya fadi cikin wata sakon murya da aike cewa jami'an tsaro suna hada baki da wasu jami'an kasashen waje da ake kyautata zaton suna yi wa Amurka aiki ne don saba umurnin da kotun Najeriya ta bayar," a cewar sanarwar.

"Muna kira ga kasashen duniya da mutane masu mutunta dan adam musamman wadanda suka taimaka aka bawa Sheikh daman zuwa India domin duba lafiyarsa su taimaka su hana gwamnatin Najeriya da na Amurka makircin da su keyi na neman halaka shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel