Firimiya ya na hannun Man City, Liverpool ko Tottenham - Mourinho

Firimiya ya na hannun Man City, Liverpool ko Tottenham - Mourinho

Tsohon Kocin da ya horar da kungiyoyin Manchester United da kuma Chelsea, Jose Mourinho, ya fadi kulob din da ya ke ganin zai lashe gasar Firimiya na Ingila a kakar wasan shekarar bana.

Fitaccen Kocin ya na ganin cewa a cikin tsofaffin kungiyoyin da ya horas watau Manchester United da kuma Chelsea, babu wanda zai iya samun nasarar lashe gasar na Firimiya a 2020.

Jose Mourinho, a na sa ra’ayin ya na ganin cewa sahun ‘Yan wasan Man City da ke benci sun fi karfin masu bugawa Man Utd da Chelsea, kuma sai su lashe gasar kafin wadannan kungiyoyi.

Da ‘yan jaridar Sky Sports su ka tambayi Jose Mourinho a kan wanda ya ke ganin za su ci kofin EPL bana, sai ya ce: “Manchester City, Tottenham, Liverpool da kuma Manchester City B”

KU KARANTA: Rashford ya yi wa Lampard tabo a wasansa na farko a Old Trafford

Duka kungiyoyin biyu su na fama ne da sababbin Matasan masu horaswa da yanzu su ka shigo gari watau Ole Gunnar Solskjaer da Frank Lampard wanda duk sun taba bugawa kulob din su.

Mourinho ya na ganin duk irin kokarin da Manchester United da Chelsea za su yi a wannan shekarar, babu yadda za a yi su doke Man City da sauran manyan Zakaru wajen cin gasar EPL.

Kocin Man Utd Ole Solskjaer ya saye ‘yan wasan baya ne irinsu Harry Maguire da Aaron Wan-Bissaka, yayin da Frank Lampard ya ke fama da haramtawa Chelsea sayen ‘yan wasa a Duniya.

Gary Neville da Graeme Souness wanda manyan Masanan kwallo ne a Ingila, sun bayyana cewa babu inda United or Chelsea za su kai a bana. A wasan farko kuwa United din ta dirki Chelsea.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel