An karrama gwamnan Kaduna da babbar Sarauta a yayin bikin babbar Sallah

An karrama gwamnan Kaduna da babbar Sarauta a yayin bikin babbar Sallah

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya samu wata babbar sarauta daga masarautar Kagarko dake karkashin jagorancin Sarkin Kagarko, Alhaji Sa’ad Abubakar, inji rahoton NAN.

Mai martaba Sarki ya nada gwamnan sarautar ‘Sadaukin Kagarko’, kuma a ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta aka yi bikin nadinsa sarautar a fadar mai martaba Sarki bayan kammal sallar Idi.

KU KARANTA: Tabbatar da zaman lafiya da sauran sakonni 6 da Buhari ya yi a jawabansa na goro Sallah

An karrama gwamnan Kaduna da babbar Sarauta a yayin bikin babbar Sallah
Sadaukin Kauru
Asali: Facebook

Sarki Sa’ad ya bayyana cewa masarautar ta ga da cewa nada Gwamna El-Rufai sarautar ne sakamakon muhimmiyar rawar da yake takawa wajen kawo cigaba mai daurewa a masarautar dama jahar gaba daya.

A cewar Sarkin, manya da kananan ayyukan da gwamnan ke gudanarwa sun amfani jama’a da dama dake jahar Kaduna, ciki har da karamar hukumar Kagarko, don haka suka ga dacewar saka ma gwamnan da wannan muhimmin sarauta.

Shim a nasa jawabin, gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana godiyarsa ga jama’an yankin saboda wannan karramawa da suka nuna masa, inda yace hakan zai kara masa kaimin gudana da aikinsa yadda ya kamata.

Daga karshe gwamnan ya yi alkawarin gina sabbin hanyoyi a karamar hukumar Kagarko, cibiyar motsa jiki da wasanni, da kuma samar da wani reshe na kamfanin sarrafa abincin dabbobi na Olams a garin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel