Hatsarin Mota: Mutane 11 sun mutu a Zamfara a ranar jajibirin Sallah

Hatsarin Mota: Mutane 11 sun mutu a Zamfara a ranar jajibirin Sallah

- Mummunan hatsarin mota ya ya yi sanadiyar rasuwar mutane 11 a Jihar Zamfara a hanyarsu na zuwa karamar hukumar Shinkafi don bikin Sallah

- Matafiyar 11 da ke cikin mota kirar Sharon duk sun mutu nan take bayan motarsu tayi karo da wata trela

- Gwamna Bello Mutawalle ya ziyarci inda hatsarin ya afku ya bayar da umurnin kwashe gawarwakin don yi musu jana'iza

A kalla mutane 11 sun mutu a ranar Asabar yayin wani mummunan hatsarin mota da ya faru tsakanin wata mota kirar Sharon da Trela a garin Damba da ke kilomita hudu kudancin Gusau babban birnin jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Abun kunya: Dan majalisar PDP ya yi wa wata mata zigidir a bainar jama'a

Mazauna garin sun shaidawa Daily Trust cewa Sharon din mai dauke da mutane 11 daga Abuja a hanyarta zuwa kauyen Jangeru a karamar hukumar Shinkafi na jihar tayi karo ne da wata trela da ke fitowa daga Gusau

"Fasinjojin da ke cikin Sharon din suna hanyarsu na zuwa yin bikin Babbar Sallh ne amma hatsarin ya ritsa da su. Babu wanda ya yi rai a cikinsu. Dukkan sun mutu nan take. Daga bisani an tafi da gawarwakin su Cibiyar Lafiya na Tarayya da ke Gusau," a cewar wani mazaunin kauyen, Sani Aliyu.

Direkta Janar na watsa labarai na gidan gwamnatin Zamfara, Alhaji Yusud Idris ya shaidawa majiyar legit.ng cewa Gwamna Bello Mutawalle na jihar ya ziyarci inda hatsarin ya faru kuma ya bayar da umurnin a dauke gawarwakin domin yi musu jana'iza.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel