Yanzu Yanzu: Jam’iyyar AAC ta dakatar da Sowore da wasu 28
Jam’iyyar African Action Alliance (AAC) ta dakatar da shugabanta na kasa, Mista Omoyele Sowore daga jam’iyyar.
Haka zalika lamarin ya shafi wasu jami’an jam’iyyar na kasa su 28.
Jam’iyyar ta dauki matakin ne a wajen babban taronta na kasa da ke gudana a yanzu haka a Rockview Hotel, Owerri.
An maye gurbin Sowore da Dr. Leonard Nzenwa.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince wa hukumar yan sandan farin kaya (DSS) da ta tsare Omoyele Sowore na tsawon kwanaki 45. An kama Sowore a ranar Asabar da ya gabata gabannin zanga-zangar juyin juya hali.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: EFCC ta sake kama surukin Atiku da lauyansa
Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, Justis Taiwo Taiwo, yace zai bari hukumar ta tsare Sowore na tsawon kwanaki 45 a karon farko, wanda ana iya sabonta shi idan an nemi hakan, domin ba DSS damar kammala bincikenta.
A karar da DSS ta shigar, karkashin sashi na 27 na dokar hana ta’addanci, hukumar ta zargi Sowore da aikata ta’addanci.
Ta kuma gabatar da faifan bidiyo biyu, wanda ke dauke da rikodin haduwar Sowore da Nnamdi Kanu, Shugaban kungiyar masu fafutukar neman yankin Biyafara da kuma wata hira inda Sowore yace mamboin kungiyar Shi’a ma za su hada hannu da shi wajen durkusar da gwamnatin Najeriya.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng