Yar Najeriya Musulma za ta kafa tarihin da ba’a taba samu ba a kasar Amurka
Wata Mata yar Najeriya kuma Musulma, Zulfat Suara nag aba da kafa tarihi a kasar Amurka, idan har ta lashe zaben maimaici da za’a gudanar a ranar 12 ga watan Satumba na majalisar dokokin jahar Tennessee.
Jaridar Guardin ta ruwaito idan Zulfat ta lashe wannan zabe inda za ta wakilci yankin Nashville, za ta zamo Musulma ta farko yar Najeriya da ta fara shiga majalisar dokokin jahar Tennessee.
KU KARANTA: Rundunar Yansanda ta yi ma rundunar Soji tambayoyin kurilla guda 5 game da kisan jami’anta
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Nashville ne babban birnin jahar Tennessee, kuma Zulfat za ta fafata ne da dan majalisa mai ci, Bob Mendes, sai dai Zulfat tace mutane da dama basu dauketa da muhimmanci ba a zaben, amma sai ga shi ta basu mamaki bayan zaben farko da aka yi a ranar 1 ga watan Agusta.
A shekarar 1993 ta koma da zama a jahar Tennessee a lokacin da mijinta ya samu gurbin kara karatu a Vanderbilt, kuma a yanzu tana da goyon bayan jiga jigan yan siyasan Tennessee da suka hada da Sanatan jahar, Brenda Gilmore, da The Tennessee Tribune, Renata Soto da Ketch Secor.
“An dade ana tsanata kamar yadda ake ma duk wani Musulmi da bakar fata, amma tsanar ta karu a kaina tun bayan da sanar da takarata, har wani ma yace zasu bindigeni, kuma mutane 2000 suka watsa wannan rubutu, daga nan na san lamarin ya girmama.” Inji ta.
Sai dai duk da haka Zulfata bata fasa aikin da take yi na kulla kyakkyawan alaka tsakanin Musulmai da wadanda Musulmai ba a jahar, inda take daga cikin jagororin kungiyar Musulmai yan Amurka, wanda suke kare hakkin Musulmai.
Haka zaika Zulfata kwararriyar akanta ce, wanda ta samu lambar yabo daga shugaban hukumar tsaro ta Amurka, FBI a shekarar 2015 sakamakon aikin da take yi da wata kungiyarta mai suna Hardeman County Junior Achievement Program, kuma ita ce tsohuwar shugabar kungiyar mata yan kasuwa na Tennessee.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng