An fitar da sunaye da hotunan 'Yan sanda 3 da sojoji suka bindige a Taraba

An fitar da sunaye da hotunan 'Yan sanda 3 da sojoji suka bindige a Taraba

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta fitar da sunaye da hotunan jami'an ta uku da sojoji suka bindige a jihar Taraba.

Mai magana da yawun rundunar, Frank Mba ne ya sanar da mumunnar lamarin a ranar Laraba inda ya bayar da labarin yadda wasu sojoji suka bude wa jami'an 'yan sandan wuta a hanyar Ibi - Jalingo a jihar.

Sunayen jami'an 'yan sandan da suka riga mu gidan gaskiya sune: Saja Usman Danazumi, Saja Dahiru Musa da Sufeta Mark Ediale.

Mba ya ce jami'an 'Yan sandan sun je Taraba ne domin kamo wani da ake zargi mai laifi ne mai suna Alhaji Hamisu. Ya ce ana zargin Hamisu da hannu cikin sace mutane don karbar kudin fansa a jihar kuma sojojin sun saki shi bayan sun kaiwa 'yan sandan hari.

A bangarenta, Rundunar Sojojin Najeriya ta ce sojojin sun yi tsamanin 'yan sandan masu garkuwa da mutane ne.

A sakon da ta wallafa a shafin ta na Twitter a ranar Alhamis, Rundunar 'Yan sandan ta fiyar da sunayen jami'anta da aka kashe a bakin aikinsu.

DUBA WANNAN: 'Na gaji da fyade da miji ne ke yi min', inji wata mata da ke neman kotu ta raba aurenta

A halin yanzu dai an kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin mataimakin sufetan 'yan sanda domin gano ainihin abinda ya faru da ya yi sanadiyar rasuwar 'yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel