An yi turereniya wajen kwasan wasu miliyoyin kudi da suka antayo daga cikin Motar banki

An yi turereniya wajen kwasan wasu miliyoyin kudi da suka antayo daga cikin Motar banki

Jama’a a jahar Georgia ta kasar Amurka sun yi rububin wasu makudan kudade da suka kai naira miliyan 62 da suka fado daga cikin wata motar banki yayin da take tafiya a kan titi, inji rahoton jaridar Fox News.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani jami’in Dansandan Dunwoody, Sajan Robert ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a da misalin karfe 8 na daren Talata, 6 ga watan Agusta, inda aka hangi takardun kudi suna yawo a saman iska.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kai harin kunar baki wake jahar Borno, 3 sun mutu

An yi turereniya wajen kwasan wasu miliyoyin kudi da suka antayo daga cikin Motar banki
Kudin
Asali: Facebook

Sajan Robert yace akalla direbobi 15 ne suka faka motocinsu, suka bazama kan titin suna wawason kudaden, daga nan kuma kowa ya shiga motarsa ya kara wuta, koda Yansanda suka iso wajen, sun tarar da motar bankin a gefen hanya, da kuma wasu yan kudi kalilan dake kan titin.

“Jami’an bankin dake cikin motar sun bayyana cewa kofar motarsu ce ta bude ba tare da sun ankara ba, wannan shine dalilin da yasa baduran kudi suka fado kan titi, sai dai sun ce basu tabbacin takamaimen adadin kudi, amma zasu kai dala dubu 175 (N62,000,0000) kenan.

“Duk da cewa mun san hatsari ne, amma fa wannan ma sata ne, don haka muke kira ga dukkanin wadanda suka kwashi kudaden su dawo dasu. Mun yi sa’a ba’a samu hadarin ababen hawa a kan titin a yayin wawason kudin ba.” Inji shi.

Sai dai a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta rundunar Yansandan Dunwoody sun tabbatar da cewa wasu muatne sun fara dawowa da kudaden da suka kwasa a yayin hadarin, daga karshe Yansanda sun kara kira ga sauran jama’an da basu dawo da kudin ba dasu taimaka su dawo dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng