An hana wata mata zaman majalisa yayin da ta shigo da jaririya rike a hannunta (Hotuna)
Majalisar dokokin Kenya ta umarci Zulekha Hassan ta fita daga cikin majalisar a dalilin shigowa da tayi rike da jaririyarta ranar Laraba.
KU KARANTA:Ni ne nan jagoran ‘inconclusive’ – Ganduje
Zulekha Hassan na daya daga cikin mambobin majalisar dokokin Kenya. Kakakin majalisar, Hon. Chris Omulele ya bayyana wannan abinda Zulekha tayi a matsayin sabawa doka.
Matar wadda take wakiltar matan Kwale a majalisar ta ce, akwai uzurin da take da shi na gaggawa wanda ya sanyata zuwa da jariryar har cikin majalisa.
“ Nayi kokarin zuwa ba tare da diyata ba, amma hakan bai yiwu ba saboda uzurin da nake da shi. Me ya kamata nayi a cikin wannan halin? Da ace akwai dakin renon yara a nan cikin majalisa ai da na kai diyata can.” A cewar Zulekha.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng