Tafiya Indiya jinya: Ana shiryawa Zakzaky da matarsa sabon fasfot

Tafiya Indiya jinya: Ana shiryawa Zakzaky da matarsa sabon fasfot

Shugaban kungiyar IMN wanda aka fi sani da Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, da uwargidarsa, Zeenat, sun fara shirye-shiryen samun sabon fasfot na fita daga Najeriya domin zuwa kasar Indiya jinya, Daily Trtust ta bada rahoto.

Majiya mai karfi ya bayyana cewa fasfot din Sheik Zakzaky da Matarsa sun kone a lokacin rikicin da ya barke tsakanin yan Shi'a da Sojoji a watan Disamban 2015.

Mayiyar yace: "Suna samun fasfot dinsu zasu samu bizan zuwa Indiya."

Hakazalika, hukumar tsaron leken asiri DSS ta ce tana cigaba da kokarin cewa ta bi umurinn kotu na barinsa ya fita asar Indiya jinya.

Kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya bayyanawa manema labarai a daren jiya cewa ana tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin bin umurnin kotu.

KU KARANTA: Abu 5 da ya kamata ku sani a kan asibitin da za a kai Zakzaky a kasar Indiya

A ranar litinin, 05 ga watan Agusta, ne wata babbar kotun jihar Kaduna ta bayar da belin shugaba 'yaan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, domin ya fita kasar Indiya a duba lafiyarsa, kamar yadda lauyoyinsa suka bukata.

Kotun ta gindaya sharadin cewa jami'an tsaron gwamnatin Najeriya ne zasu raka Zakzaky zuwa asibitin na kasar Indiya domin su tiso keyarsa ya dawo Najeriya da zarar ya warke.

Mabiya shugaban sun bayyana cewa El-Zakzaky ya samu shanyewar barin jikinsa kuma ya rasa ido daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel