Zanga-zangar juyin juya hali: Buhari na kokarin mai damu baya zuwa 1948 – Falana

Zanga-zangar juyin juya hali: Buhari na kokarin mai damu baya zuwa 1948 – Falana

-Femi Falana ya kalubalanci Shugaba Buhari a kan zanga-zangar juyin-juya hali

-Lauyan ya ce wannan zanga-zangar na nan a ciki dokar kasa saboda ba ta daya daga cikin ababen da kundin tsarin mulkin Najeriya haramta

-A lokacin da kayi naka zanga-zangar an saurareka saboda yanzu zaka hana wasu suyi, a cewar Falana zuwa ga Buhari

Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana (SAN) a ranar Talata ya ce Shugaba Muhammadu Buhari na kokarin mayar da Najeriya baya zuwa lokacin da babu ‘yanci, saboda yinkurinsa na dakile zanga-zangar lumana wadda dokar kasa ta hana ba.

Falana yayi wannan furucin a cikin wata hirar talabijin da akayi da shi a Abuja, inda yake cewa: “ Lokaci na karshe da muka ga irin wannan abu shi ne a shekarar 1948, yayin da kungiyar Zikist ta soma irin wannan zanga-zangar ta juyin juya hali.

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya za ta gina sabbin dakunan gwaje-gwajen kimiyya a Jami’o'i shida

Ko wancan lokacin ba a kirasu da sunan masu shirin hambarar da gwamnati ba. A shekarar 1993 ne Kotu daukaka karat a haramta irin wannan aiki a karkashin dokar Criminal Code. Amma kuma ko wane dan Najeriya yana da yancin fadin ra’ayinsa.”

A cewar Lauyan mai fafutukar kare hakkin bil adama: “ A shekarar 2011, Janar Buhari yayi kokarin kawo irin halin hambarar da gwamnatin kasar Masar zuwa nan Najeriya. Yanzu kuma ga shi yana bisa mulki ana masa zanga-zanga.

“ Abinda ‘yan Najeriya ke kira a yanzu kawai shi ne dole gwamnati ta maida hankali wurin gudanar da ayyukanta, hard a yan kungiyar dimokurradiyya ta kasa na cikin zanga-zangar wato NADECO.

“ Har yanzu ban manta, zanga-zangar da APC ta shirya a shekarar 2014 ba inda take kalubalantar rashin tsaro. Dalilin rashin tsaron ne ya sanya yanzu ma ake wannan zanga-zangar. Ba zaka iya hanasu yin zanga-zangar ya zama dole ka sauraresu saboda kaima an saurareka a wancan lokacin.” Inji Falana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel