Ambaliyar ruwa ta kashe mutum daya, ta kuma lalata gidaje fiye da 100 a Bauchi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum daya, ta kuma lalata gidaje fiye da 100 a Bauchi

Ambaliyar ruwa da ya faru sakamakon ruwan sama mai karfi ya yi sanadiyar rasuwar mutum daya tare da shafe gidaje fiye da 100 a kauyukan Dindima da Liman Katagum da ke karamar hukumar Bauchi.

Kauyukan da ambaliyar ta faru duk galibinsu kananan manoma ne da suka rasa muhallansu da kayayakin su sakamakon ambaliyar ruwar.

Dagacin Dindima, Malam Sale Ubandoma ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce mutum daya ya mutu yayin da fiye da gidaje 100 ambaliyar ta shafa.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: PDP ta dakatar da shugabaninta 5 da wasu mutane 9 a Kebbi

Sai dai gwamnan jihar, Bala Muhammed ya yi alkawarin sake gina gidajen da ambaliyar da shafe.

Gwamnan da ya samu wakilcin Kakakin Majalisar Jihar Bauchi, Hon Abubakar Suleiman ya ziyarci kauyukan domin jajantawa wadanda abin ya shafa.

Ya bawa Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa na Jihar (SEMA) ta gaggauta kai dauki ga al'ummar jihar ta hanyar tabbatar da samar musu kayyakin more rayuwa da tallafi.

Ya yi alkawarin gyara gadan da ke garin cikin kankanin lokaci saboda mazauna kauyan su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel