Jerin sunaye: PDP ta dakatar da shugabaninta 5 da wasu mutane 9 a Kebbi

Jerin sunaye: PDP ta dakatar da shugabaninta 5 da wasu mutane 9 a Kebbi

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da shugabanin ta na kananan hukumomi buyar da wasu mutane tara saboda yi wa jam'iyya zagon kasa.

Sanarwar ta shugaban jam'iyyar na jihar, Mallam Haruna Saidu ya bayar ranar Talata a Birnin Kebbi ya ce ana zargin 'yan majalisar ne da kunyatta jam'iyyar da shugabaninta da bata wa jam'iyyar suna.

Ya yi bayanin cewa 'yan jam'iyyar 14 da aka dakatar sun saba dokokin jam'iyyar da shugabanin ta.

Saidu ya kuma yi ikirarin cewa sun yi ta yadda karerayi da bata sunan shugabanin jam'iyyar yada kiyaya tsakanin 'yan jam'iyyar na jihar.

DUBA WANNAN: An bindige shugaban wata kungiyar 'yan kasuwa a Zakibiam

Ya lissafa sunayen wadanda aka dakatar kamar haka: Nuhu Goma, Shugaban PDP na karamar hukumar Zuru, Aminu Sawwa, Shugaban PDP na karamar hukumar Argungu; Abubakar Kudu; Shugaban PDP na karamar hukumar Maiyam; Bello Bunza, Shugaban PDP na karamar hukumar Bunza; Bello Gulmare, Shugaban PDP na karamar hukumar Gwandu.

Saura sun hada da Alhaji Ibrahim Manzo; Mataimakin shugaban jam'iyyar ta Kebbi Central, Alhaji Abubakar Basse; Muhammadu Ruwa, Mataimakin shugaban jam'iyyar Kebbi North, Isiyaku Dauda, and Udulu Manpower, mukadashin mai bayar da shawara ta fanin shari'a.

Sauran sun hada da Yalli Jega, Shuganan mata na Kebbi Central, Isah Gwandu, mataimakin ma'aji da Joshua Bamaiyi,” inji shi.

Shugaban jam'iyyar ya ce an dakatar da 'yan jam'iyyar 14 ne na tsawon watanni uku yayin da za a gudanar da bincike kuma a saurari shawara daga kwamitin zartarwa na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel