Zanga-zangar juyin juya hali: Sowore ya ce a ci gaba da gashi

Zanga-zangar juyin juya hali: Sowore ya ce a ci gaba da gashi

Mai wallafa labarai a shafin Sahara Reporters kuma mai fafutuka, Omoyele Sowore wanda hukamar tsaro ta farin kaya, (DSS) ta kama a makon da ya gabata, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ci gaba da zanga-zangar juyin juya hali.

Mista Sowore ya bayyana hakan ne ga abokan fafutukarsa da suka ziyarce a wajen da yake tsare, da yammacin ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta rahoto.

Ya ce: "Ina farin ciki yadda zanga-zangar lumana ta juyin juya hali ta kasance."

A safiyar ranar Litinin ne dai masu zanga-zangar juyi njuya haki suka fantsama kan titunan wasu jihohi domin fara gudanar da gangaminsu wanda suka shirya yi na tsawon 'yan kwanaki, sai dai da alama abubuwa ba su faru yadda suka so ba.

A cikin makon da ya gabata an kama babban jagoran zanga-zangar wato Omoyele Sowore.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar juyin hali: An zuba manyan jami’an tsaro a sabon wajen taron na Lagas

Mai magana da yawun hukumar DSS ya bayyana cewa suke da alhakin kama shi sakamakon zarginsa da ake yi na yunkurin hambarar da gwamnati mai ci a kasar.

Omoyele Sowore dai ya yi takarar shugaban kasar Najeriya a zaben da ta gabata kuma shi ne ya shirya zanga-zangar da ya kamata ya faru a cikin jihohi 21 na cikin jihohi 36 na kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel