Yanzu-yanzu: Obasanjo yana ganawar sirri da shugabanin kungiyoyin Fulani

Yanzu-yanzu: Obasanjo yana ganawar sirri da shugabanin kungiyoyin Fulani

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya na ganawa da shugabanin kungiyoyin Fulani da ke zaune a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

An kira taron ne domin warware matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankin da galibi ake zargin fulani da alhakin kai hare-hare.

Shugabanin Fulanin sun isa wurin taron ne karkashin jagorancin, Saleh Bayeri, shugaban kungiyar Gan Allah Fulani Association da wasu shugabani uku da ke wakiltan jihohin Kudu maso Yamma da jihar Kogi.

DUBA WANNAN: Shahararrun 'yan wasa 15 da ba su taba buga wa kasarsu ta haihuwa kwallo ba

Obasanjo ya iso wurin taron tare da wani da aka ce makiyaya sun taba kai wa hari.

A jawabinsa na bude taro kafin su kebe, Obasanjo ya shawarci mahalarta taron su fadi dukkan abinda ke zuciyarsu domin hakan ne kawai za a samu maslaha

"Ina rokon ku da kada ku bar wani abu a zuciyarku, ta hakan ne kawai za mu iya samun nasara a wannan taron.

"Dukkan mu mun san halin da kasar ke ciki na rashin tsaro. Ya kamata su nemo hanyoyin warware matsalar," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel