Ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar rasuwar kananan yara 4 a Yola

Ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar rasuwar kananan yara 4 a Yola

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA) ta ce rasuwar wasu mutane biyar ciki har da jariri sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a Yola babban birnin jihar Adamawa.

Dakta Mohammed Sulaiman, babban sakataren hukumar ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a ranar Juma'a a Yola.

Suleiman ya yi bayanin cewa lamarin ya faru ne a daren Alhamis bayan ruwa da aka yi kamar da bakin kwarya a wasu sassan jihar.

A cewarsa, anyi asarar kayayakin miliyoyin naira sakamakon ambaliyar ruwan.

DUBA WANNAN: An gano wasu kayan talakwa dan takarar zama ministan Buhari ya yi sama da fadi da su (Hotuna)

Ya ce an tura jami'an hukumar zuwa wuraren da abin ya faru domin tallafa musu tare da nazarin irin asarar da aka yi.

"Ambaliyar ruwar ya kashe mutane biyar, hudu daga cikinsu yara ne sakamakon ruwan sama mai karfi da akayi a jiya (1 ga watan Yuli) a garin Yola da kewaye.

"An rasa kadarorin miliyoyin naira," a cewar Sulaiman.

Ya ce hukumar tana tuntubar hukumomn da suka da alhakin taimakawa mutanen abinda ya faru.

Ya ce garuruwan abin ya shafa sun hada Yolde-Pate, Damare, Wuro-Jabbe, Damilu da Jambutu a kananan hukumomin Yola ta Kudu da Yola ta Arewa.

Malam Kabiru Bello, wani mazaunin garin Wuro Jabbe a karamar hukumar Yola ta Kudu ya ce ya rasa yara biyu sakamakon ambaliyar ruwa.

Bello ya kuma ce makwabcinsa shima ya rasa yara biyu ciki har da jariri dan watanni 10.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel