Direban Dangote ya tseratar da daruruwan dalibai daga rikicin kabilanci a jahar Taraba

Direban Dangote ya tseratar da daruruwan dalibai daga rikicin kabilanci a jahar Taraba

Wani direban Dangote ya yi bajinta bayan ya tseratar da daruruwan dalibai daga wani yanki a jahar Taraba da ake fama da kazamin rikicin kabilanci tsakanin Tibabe da Jukunawa, inji rahoton Benue Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Direban da ba’a bayyana sunansa ba ya kwashe daliban jahar Benuwe ne dake karatu a jami’ar gwamnatin tarayya ta Wukari, jahar Taraba, a daidai lokacin da rikicin kabilanci ya dabaibaye garin Wukarin.

KU KARANTA: Majalisar Musulunci ta koli yi karin haske game da ganin watan Zulhijja

Direban Dangote ya tseratar da daruruwan dalibai daga rikicin kabilanci a jahar Taraba
Direban Dangote
Asali: Facebook

Sai dai majiyar ta tabbatar da cewa wannan direba dan albarka gaban kansa ya yi, kuma ba hukuma bace ko kamfaninsa ta aikoshi ba, a’a, gani kawai ya yi ya kamata ya taimaka ma daliban da rikicin ya rutsa dasu domin su tsira daga sharrin maharani kabilun biyu.

Wannan kyawun hali da wannan bawan Allah Ya nuna ya yi matukar faranta ma yan Najeriya rai daga kowanne bangare da addini, inda jama’a da dama suke shi masa albarka tare da fatan cigaba da samun ire irensa a Najeriya.

A wani labarin kuma, Alhaji Aliko Dangote ya dauki alkawarin daukan zakakuran daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta jahar Kano aiki a kamfanoninsa, kamar yadda shugaban jami’ar Farfesa Shehu Alhaji ya bayyana.

Farfesa Shehu ya bayyana cewa Dangote zai dauki daliban jami’ar da suka kammala digiri da maki mafi daraja (First Class) da mabi dashi (2:1) daga fannonin aikin injiniya, kimiyyar zane zane, da kuma noma.

Bugu da kari attajirin dan kasuwan ya yi alkawarin janyo babban layin wutar lantarki zuwa jami’ar domin samar da isashshen wutar lantarki a jami’ar don saukaka karatun dalibai da sauran ayyukan jami’ar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel