Yadda saurayi ya makure budurwarsa har lahira a Otel bayan sun gama soye wa

Yadda saurayi ya makure budurwarsa har lahira a Otel bayan sun gama soye wa

Wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya makure wata wata mata mai suna Maureen har sai da ta mutu bayan sun gama saduwa a wani Otel da ke Fatakwal.

Lamarin ya faru ne a layin Peremabiri da ke D-Line a birnin Fatakwal.

Rahotanni sun nuna cewa Maureen da ake kyautata zaton budurwar mutumin ne ta kama dakin Otel din ne a ranar Laraba kafin daga bisani wani mutumin da ba a gano ko wanene ba ya tarar da ita a Otel din kuma daga bisani ya sulale ya tsere bayan ya kashe ta.

DUBA WANNAN: Tsaro: Gwamnonin Arewa sun yafe wa 'yan bindiga da barayin shanu

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni ya ce binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa saurayin ya makure ta ne bayan sun gama saduwa.

Omoni ya kara da cewa, "Mun kuma gano wani abu mai muhimmanci mallakin mutumin da ya manta da shi kafin ya tsere."

A baya, Legit.ng ta kawo muku cewa wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a dakin kwanan dalibai mata na Jami'ar Uyo a daren ranar Laraba inda suka yi awon gaba da kudaden dalibai da wasu abubuwa masu muhimmanci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun bi daki zuwa daki suna amshe wa daliban kayayakin su.

Wani a jami'an da ya nemi a boye sunansa ya ce duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, wasu dalibai sun jikkata yayin da su kayi kokarin tserewa.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Macdon Odiko ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Alhamis, ya kuma ce Kwamishinan 'yan sandan jihar, zaki Ahmed ya bayar da umurnin girke 'yan sanda domin gadin dakunnan daliban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel