Tsaro: Gwamnonin Arewa sun yafe wa 'yan bindiga da barayin shanu

Tsaro: Gwamnonin Arewa sun yafe wa 'yan bindiga da barayin shanu

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce gwamnonin Arewa maso Yamma sun yi wa 'yan bindiga da barayin shanu afuwa saboda yunkurin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a yankin.

Masari ya bayyana hakan ne cikin rahoton bayan taro da aka karanta a karshen taron tsaro da sulhu na kwana guda da aka gudanar tare da jami'an tsaro, da 'yan kungiyar sa kai da makiyaya da manoma a ranar Alhamis a Katsina.

"Daga yau, kada wani dan banga ko dan kungiyar sa kai ya sake kaiwa makiyaya hari ko kashe su saboda ya zama dole ayi dukkan bangarorin suyi hakuri domin a samu zaman lafiya mai dorewa.

"A kyalle makiyaya da iyalansu su cigaba da harkokinsu da zuwa kasuwani da wuraren ibada ba tare da tsangawa ba muddin ba su dauke da makamai ba.

DUBA WANNAN: Zaben Kano: Kotu ta aike wa INEC da Kwamishinan 'Yan sanda sammaci

"'Yan bindigan da suka sace shanu daga kauyuka su mayar da su wurin gwamnati ko su kaiwa kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah.

"'Yan bindiga sun ajiye makamansu sannan su saki dukkan mutanen da suke garkuwa da su nan take.

"Muna murnan ganin cewa an saki wasu daga cikin wadand aka yi garkuwa da su a Zamfara da wasu jihohi," inji shi.

A bangarensa, Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce jihar sa za ta samarwa makiyaya filayen kiwo domin su zauna a wuri guda.

Matawalle ya ce, "Muna damuwa kan yadda makiyaya ke yawo tare da dabobinsu wadda hakan ke jefa su cikin hadurra masu yawa.

"Gwamnonin sun cimma matsaya guda, kuma ya kamata ku cimma matsaya cewa za ku dena satar dabobi, garkuwa da mutane ko kisa.

"Kuma ku saki dukkan wadanda ku kayi garkuwa da su domin ku nuna mana kun tuba."

A jawabinsa, Sufeta Janar na 'Yan sanda, Mohammed Adamu ya ce kada wanda ya sake kashe wani da sunan dan banga ko dan kungiyar sa kai.

Ya ce 'Yan sanda za su hukunta duk wanda aka samu ya kashe wani haka sidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel