'Yan sanda sun samu makudan kudin bogi a gidan dan siyasa yayin samame
'Yan sanda sun kai samae gidan wani babban dan siyasa tare da kama makudan kudin jabu.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an 'yan sandan sun kwace makudan kudin bogin, na gida da kasashen waje, a gidan dan siyasar da ke rukunin gidajen Elgon a yankin Eldoret a birnin Nairobi da ke kasar Kenya.
Kafar yada labarai ta K24 ta ce gidan da aka samu kudin bogin mallakar wani dan siyasa ne da ya fadi zaben kujerar majalisa a shekarar 2017.
A 'yan kwanakin baya bayan nan ne jami'an 'yan sanada a kasar Nairobi suka bayyana damuwarsu a kan yawaitar hada-hada da jabun kudade, wadanda ake zargin wasu manya ne ke da alhakin buga su.
Ko a kwanakin baya sai da jami'an 'yan sandan kasar suka kama wasu makudan miliyoyin kudin bogi a wani gida da ke garin Ruiru.
Wani masanin tattalin arziki a kasar ya ce ba za a iya sanin illar da kudaden bogi ke yi w tattalin arzikin kasar ba saboda rashin alkaluman kudaden jabun da aka kama.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng