Suhaila Zakzaky ta bayyana cewa yan Shi’a zasu cigaba da zanga zanga a kan tituna

Suhaila Zakzaky ta bayyana cewa yan Shi’a zasu cigaba da zanga zanga a kan tituna

Diyar shugaban yan Shia, Ibrahim Zakzaky, Suhaila Ibrahim Zakzaky ta bayyana cewa yan shia ba zasu daina gudanar da zanga zanga a kan titunan Najeriya don tilast ba gwamnati sakin mahaifinta ba, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Suhaila ta bayyana haka ne daga kasar Dubai, inda tace babu gudu babu ja da baya game da zanga zanga, don haka ta yi kira mabiya Shia dasu yi watsi da umarnin kungiyar IMN na dakatar da zanga zangar.

KU KARANTA: Jahar Akwa Ibom ta shigo da shanu 2,000 daga kasar waje don kiwatawa

A ranar Laraba, 31 ga watan Yuli ne shugaban sashin watsi labaru na kungiyar yan Shia, Ibrahim Musa ya sanar da dakatar da da duk wani zanga zanga a duk fadin Najeriya, biyo bayan haramta kungiyar da ayyukanta gaba daya da gwamnatin Najeriya ta yi.

Sai ga shi kwatsam diyar Zakzaky, Suhaila ta yi bara’a da wannan umarni cikin wani bidiyo da ta fitar a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, inda ta nemi yan Shia kada su bi umarnin kungiyar, sa’annan su koma kan titi su cigaba da zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja.

Suhaila ta kara da cewa kungiyar Shia bata da wani mai magana da yawu, a cewarta Ibrahim Musa baya wakiltar kungiyar Shia, don haka umarnin dakatar da zanga zangar daya bayar ra’ayinsa ne, ba ra’ayin kungiyar Shia bane.

“Ina so in yi karin haske ne game ikirarin da wasu ke yi na cewa wai kungiyar Shia ta dakatar da gudanar da zanga zanga a garin Abuja, jama’a su sani wannan ba ra’ayin kungiyar Shia bane, kuma yan Shia zasu cigaba da zanga zanga.

“Da farko dai kungiyar Shia ba ta da wani mai magana da yawunta, don haka mutumin daya fitar da wannan sanarwa ba wani bane illa editan jaridar Al-Mizan, kuma kungiyar da yake jagoranta tamkar sauran kungiyoyin Shia ne.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel