Jahar Akwa Ibom ta shigo da shanu 2,000 daga kasar waje don kiwatawa

Jahar Akwa Ibom ta shigo da shanu 2,000 daga kasar waje don kiwatawa

Gwamnatin jahar Akwa Ibom ta sayo wasu shanu guda 2,000 daga kasar Brazil domin kiwata, a wani mataki da tace zai samar da isashshen naman miya ga jama’an jaharta.

Legit.ng ta ruwaito kwamishinan watsa labaru na jahar, Charles Udoh ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Uyo, inda yace gwamnatin ta yanke shawarar shigo da dabbobin ne don kara adadin sinadarin abinci mai gina a jiki a tsakanin jama’an jahar.

KU KARANTA: Mutane 15 sun mutu a mummunan hatsarin kwale-kwale a jahar Neja

Haka zalika kwamishina Udoh yace gwamnatin jahar ta kirkiri wasu muhimman matakan tabbatar da yalwataccen abinci da kuma tsare tsaren noma na zamani a jahar.

“Mun samar da wajen kiwon dabbobin ne tare da hadin gwiwar masu zuba jari daga kasashen waje, kuma sai da aka tantance dabbobin don gudun shigo masu dauke da cututtuka, haka zalika sai da muka shiryasu don sabawa da yanayin kasar mu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki ya lashi takobin ba zai taba bayar da koda taki daya na filin jaharsa ga gwamnatin tarayya don kafa gandun dabbobi a karkashin tsarin RUGA ba.

Obaseki wanda ya gaji Adams Oshiomhole a matsayin gwamnan jahar, amma a yanzu dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a kan kalubalen kiwon dabbobi irin na makiyaya a jahar Edo, a babban birnin tarayya Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel