Hukuncin kisa ya hau wani matashi daya kashe abokinsa a kan bashin N20 a Kano

Hukuncin kisa ya hau wani matashi daya kashe abokinsa a kan bashin N20 a Kano

Wata babbar kotun jahar Kano ta yanke hukuncin kisa a kan wani matashi dan shekara 25 mai suna Umar Yakubu bayan ta kamashi da laifin kisan abokinsa, Ibrahim Adamu a sanadiyyar rikici a kan bashin naira 20.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa kotun ta yanke ma Yakubu hukunci ne a kan tuhuma daya kwal daya shafi aikata laifin kisan kai da gangan, wanda ya saba ma sashi na 221 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Kano.

KU KARANTA: Uwargidar shugaban kasa da matan gwamnoni sun gudanar da taro a kan matsalar fyade a Landan

Da fari, lauyan masu kara, Lamido Soron Dinki ya shaida ma kotun cewa Yakubu ya kashe Adamu dan shekara 22 ne a ranar 13 ga watan Yunin shekarar 2018 da misalin karfe 11 na safe a unguwar Sabuwar Gandu.

“A wannan rana Yakubu ya roki Adamu ya bashi rancen naira 20, daga nan ne kawai sai cacar baki ta kaure a tsakaninsu, inda nan take Yakubu ya ciro almakashi ya sossoka ma Adamu a kirjinsa, inda nan take ya fadi matacce.” Inji shi.

Bugu da kari, majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin zaman, Lauya Soron Dinki ya gabatar da shaidu kwarara guda 6, wadanda kotu ta aminta dasu, yayin da shi kuma Yakubu wanda ake kara ya gaza kawo ma kotu shaida ko daya.

Da wannan ne Alkalin kotun, mai sharia Dije Aboki ta tabbatar da cewa masu kara sun gabatar da gamsassun jawabai ma kotu, kuma kotu ta gamsu dasu, don haka ta yanke ma Yakubu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel