Tsaro: An murkushe Boko Haram na asali da muka sani - Hadimin Buhari

Tsaro: An murkushe Boko Haram na asali da muka sani - Hadimin Buhari

Fadar shugaban kasar Najeriya da ta ce tana nan kan bakar ta na cewa anyi nasarar cin kungiyar Boko Haram da yaki duk da irin hare-haren da 'yan ta'addan suka kai a wasu wurare a yankin na Arewa maso Gabashin Kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasar Mallam Garba Shehu ne ya sanar da hakan cikin wata jawabi da ya fitar a ranar Talata.

Ya ce, "Matsayin gwamnatin Najeriya shine a ci galaba kan Boko Haram kuma an murkushe su. Ainihin Boko Haram da muka sani, an ci su da yaki.

"Abinda muke da shi yanzu shine 'yan tsiraru da su kayi saura, masu laifi da suka tsere, 'yan ta'addan kungiyar AQIM da sauran 'yan ta'addan Afirka da ke hada kan."

DUBA WANNAN: Hajjin Bana: Maniyyatan Najeriya biyar sun rasu a Saudiyya

"Hakan ya faru ne sakamakon rushewar kasar Libya da kuma kasashen Iraqi, Syria da Lebanon. Suna kwararowa kasashen mu ne saboda rashin ingantaccen tsaro a iyakokin mu na kasashen Afirka".

Ya ce an samu karin shigowar haramtattun makamai ta iyakokin kasar musamman daga yankin Tafkin Chadi sakamakon samuwar wadannan kungiyoyin na kasa da kasa.

A cewar Shehu, ana fama da irin wadannan matsalolin a kasahen Nijar, Mali, Chadi da Kamaru kuma abin yayi muni ne saboda girmar da Najeriya da shi na kimamin fadin sakwaya kilomita miliyan daya.

Hadimin shugaban kasar ya ce an samu cigaba sosai a fanin tsaro karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari idan aka kwatanta da yadda ya tarar da kasar.

Ya ce Boko Haram suna kai hare-hare a kusan rabin jihohin Najeriya a shekarar 2015 da Shugaba Buhari ya karbi mulki amma yanzu abin ya takaita ga wasu tsirarun wurare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel