Babbar magana: Atiku, mahaifinsa da kakansa duk 'yan kasar Kamaru ne - Shaidar Buhari ya fada wa kotu

Babbar magana: Atiku, mahaifinsa da kakansa duk 'yan kasar Kamaru ne - Shaidar Buhari ya fada wa kotu

Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shaida wa kotun sauraronn korafin zaben shugaban kasa cewa dan takarar shugaban kasa a karekashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, dan asalin kasar Kamaru ne 'jini da tsoka'.

Kyari, wanda Cif Wole Olanipekun, lauyan shugaba Buhari, ya jagoranta zuwa wurin tsayawar shaida a gaban kotun ranar Talata, ya kafe kan cewa Jada, garin da aka haifi Atiku, na karkashin arewacin kasar Kamaru ne a shekarar 1946 da aka haifi Atiku.

Ya bayyana cewa an haifi Atiku ne a shekarar 1946 kafin a gudanar da kuri'ar raba gardama da ta dawo da wasu sassan gabashin kasar Kamaru cikin Najeriya a shekarar 1961.

Shaidar ya ce tsarin mallaka na kasar Faransa ya tilasta mutanen Jada har da Atiku da mahaifinsa da kakansa zama 'yan asalin kasar Kamaru 'tsoka da jini'.

Dangane da batun takardun karatun shugaba Buhari, Kyari ya ce shine da kansa ya je jami'ar Cambridge a ranar 18 ga watan Yuli ya karbo takardar kammala makarantar sakandire ta shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel