Alamomi 5 dake nuna yawan sukari sosai a jikin dan Adam
Hukumar lafiya ta duniya WHO cikin wata sabuwar matashiyar jagora da ta fitar dangane da yadda ya dace a yi ta'ammali da sukari a kowace rana, ta ce domin neman zama cikin koshin lafiya kada mutum ya sha sukari da ya haura ma'aunin gram 25 wato karamin cokalin shan shayi 6 kacal.
Binciken da aka gudanar a kan sukari ya tabbatar da cewa, ana samun sukari ƙwarai da ya wuce bukatar jikin dan Adam cikin wasu nau'ikan abinci da suka hadar da alewa, biskit, lemukan roba, kwalba da na gwangwani, dangogin gasashiyar fulawa da a turance ake kiran su Pastries.
Ta'ammali da wannan kayayyakin abinci na da babban hatsari ga lafiyar dan Adam kamar yadda binciken hukumar lafiya ta duniya ya tabbatar.
KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta tafi hutun shekara, za ta dawo a ranar 24 ta watan Satumba
Akwai sunadarai a cikin wasu nau'o'in abinci masu zaki amma su kan kara inganta lafiyar dan Adam. Ire-ire wannan sunadarai sun hadar da Vitamins, minirals da kuma fibre.
Ga wasu alamomi biyar da ke nuna cewa akwai sukari ƙwarai a jikin dan Adam da ya wuce misali kuma hakan yana barazana ga lafiya. Alamomin sun hadar da;
1. Nauyin jiki, teba da kuma karuwar ƙiba.
2. Kwadayi da kuma yawan nuna ƙwalama a kan nau'oin abinci masu zaƙi.
3. Bayyanar ƙurarraji a fuska, wuya, da kuma ƙirji.
4. Rashin kuzari da ƙarfin jiki.
5. Yawan ciwon haƙori.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng