Wani mutumi ya kashe yaro dan shekara 8 ta hanyar ingizashi kasan jirgin kasa.

Wani mutumi ya kashe yaro dan shekara 8 ta hanyar ingizashi kasan jirgin kasa.

Wani azzalumi ya fada hannun jami’an tsaro bayan ya kashe wani karamin yaro dan shekara 8 ta hanyar hankadashi gaban wani jirgin kasa mai tsananin gudu da ta tattake yaron har lahira, inji rahoton jaridar Blue Print.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a birnin Frankfurt na kasar Jamus, inda mutumin ya ingiza yaron tare da mahaifiyarsa kan layin dogo yayin da jirgi ke tahowa, kamar yadda kaakakin Yansandan birnin ta bayyana.

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun yi kira ga Buhari ya waiwayesu a kan nade naden mukamai

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa mutumin ya lallabo ta bayan matar da danta ne ba tare da sun sani ba, da haka yasa hannu ya hankadasu gaban jirgin, sai dai mahaifiyar yaron mai shekaru 40 ta yi kokari ta kauce ma fadawa titin jirgin, amma yaronta bai yi sa’a ba, nan take yam utu.

“Bayan ganin abinda ya aikata sai mutumin ya ranta ana kare, amma mun samu nasarar damkeshi tare da taimakon jama’an dake jiran shiga jirgi a tashan jirgin kasan, kuma a yanzu mun fara binciken dalilinsa na aikata kisan.” Inji kaakkain Yansanda.

Sakamakon aukuwar wannan lamari, an rufe layukan dogo a birnin Frankfurt, kuma an hana jiragen kasa da dama tashi, yayin wasu kuma aka jinkirta lokacin tashin nasu.

Ko a kimanin makonni uku da suka gabata an samu kwatankwacin haka inda aka jefa wata mata yar shekara 34 gaban jirgin kasa a filin jirgin kasa na Voerde, dake yammacin jahar Nothr-Rhine Westphalia, ita ma nan take ta mutu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng