Yadda wata mata ta je Makkah sannan ta gina gida da kudin kitso a Abuja

Yadda wata mata ta je Makkah sannan ta gina gida da kudin kitso a Abuja

Masu iya magana kan ce sana'a karba-karba, kuma duk kankantar ssana'a idan har Allah ya sa wa bawansa albarka ciki, sai ka ga ya kasance ccikin runfin asiri. hakan ce ta kasance da Hajiya Bilkisu Shu'aibu wacce ta fara kitso tun tana shekara 11. Ta yi shekara 26 ta na kitso.

A cikin kudin kitso take samu ta biya bukatunta.

Ta ce ta samu alfanu sosai sanadiyyar sana'ar kitson, ciki har da zuwa hajji da gina gida; “Don haka sai ina gani kamar in na bar kitso, na ci amanar kitso. Saboda ya riga yayi mun komai tun daga tashi na.

“Na shiga sana’ar tun ina shekara 11. Ni ce Bilkisu Shu’aibu mai kitso, Na yi shekara 26 ina sana’ar kitso. Tun ina karban naira 5, 10, 20, ana bani, bana rainawa. Har na zo ana bani naira 50, 100, Ba na rainawa, har na shigo Abuja. Sai na zo na ci gaba ina yi, ina yi, har Allah ya ba ni sa’a na yi adashe.

“Da na dauki adashen, sai rannan ina bacci, sai ya zo mun kamar a mafarki. Sai na ce idan, na dauki adashen nan me ya kamata na yi da shi? Sai zuciyata tace ki je hajji. Na je na biya.

“Baya ga haka, na gama da zancen hajji, na zo nace ina so na yi gida, da haka in samu dubu 10, dubu 5, a kitson ne kuma na samu har na yi gida. Ba ya ga haka, na kan taimaka wa dana ya yi karatu, don haka har ya je jami’a, yanzu yana bautar kasa.

KU KARANTA KUMA: Ban hana 'yan Shi'a yin addininsu ba – Buhari

“Har jiha-jiha ana daukata in yi kitso, in yi wa amarya in yi wa mutane, wadanda suka riga suka saba dani."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel