NAFDAC tayi gargadi kan cin ganda, ta ce tana da illoli a jikin dan adam

NAFDAC tayi gargadi kan cin ganda, ta ce tana da illoli a jikin dan adam

-Hukumar NAFDAC ta yi kashedi ga masu cin fatar dabbobi a matsayin abinci

-Darakta Janar ta hukumar ce ta bada wannan sanarwa kasancewar ana amfani da sinadarai da kan iya kawo illa a jikin dan adam wurin sarrafa fatun

-NAFDAC ta bayyana wasu daga ciki illoli da cin gandar kan iya kawowa jikin da adam a ciki hadda ciwon koda

Hukumar kula da tsaftar abinci da magunguna ta kasa wato NAFDAC ta gargadi al’umma da su guji cin fatar dabbobi wanda aka fi sani da ganda.

A wani zance da muka samu daga wurin Darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce, akasarin fatun ana sarrafasu ne domin ayyukan kamfani.

KU KARANTA:Tantance ministoci: Majalisar dattawa taje hutu takaitaccen lokaci

Adeyeye ta kara da cewa, wasu daga cikin fatun har ila yau ana sarrafasu da sinadarai iri daban-daban wadanda kan iya zama illa ga lafiyar dan adam idan ya cisu.

A cewarta, bincike ya nuna cewa wasu kamfonin kasar nan na shigowa da fatun ne daga kasashen Labnan da Turkiya, yayin da da dama ke shigo da nasu ta haramtacciyar hanyar fasa kwauri a kanya iyakar kasar nan.

Rahotanni daga Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya bamu zancen hukumar kamar haka: “ Hukumar NAFDAC a madadin dukkanin ma’aikatanta naso tayi amfani da wannan dama domin janyo hankalin al’umma kan su kiyayi cin fatar dabbobi wato ganda, kasancewar hanyar sarrafata cike take da tangarda.

“ Ana shigo da fatun kasar nan ne domi sarrafa takalma, jakunkuna, bel da wasu abubuwan masu kama da wannan. Masana ilimin kiwon lafiya sun tabbatar mana cewa cin gandar na iya haifar da cututtuka da yawa a jikin dan adam.Wadannan cututtuka sun hada da; ciwon koda, ciwon hanta, ciwon daji da dai sauransu.”

A don haka hukumar NAFDAC ke jan hankali al’umma da su lura kwarai da gaske wajen sanin abinda suke saya a matsayin abinci domin tsare lafiyar jikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel