Ba na nadamar mayar da kudi N15m da na tsinta - Kofura Bashir Umar

Ba na nadamar mayar da kudi N15m da na tsinta - Kofura Bashir Umar

Kofura Bashir Umar, wanda ya kasance dan agajin kungiyar Izalah kafin ya zama jami'in soja ya dawo da kudi Yuro 37,000, kimanin milyan 15 ga wani Alhaji Ahmed, wanda ya yarda kudin a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, 2019 a kasuwan sansanin maniyyata aikin Hajji dake jihar Kano.

Babban hafsan sojin saman Najeriya a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja ya karawa Bashir Umar, girma daga matsayin ACM zuwa Kofura. Ya bayyana cewa wannan zai zama darasi ga sauran jami'an hukumar da kuma nuna cewa hukumar sojin sama na masu gaskiya, aminci da mutunci ne.

A wani hira da jaridar Daily Trust, Bashir Umar ya bayyana yadda wasu ke sukarsa kan wannan halin kwarai da yayi.

KU KARANTA: Kasar Laberiya ta karrama shugaba Muhammadu Buhari (Hotuna)

DT: Shin ka yi tunani ajiye kudin wa kanka?

Kofura: Ban yi tunani ko na kwayar zarra in ajiye kudin ba, saboda mahaifina ya yi min tarbiyyar kada in taba dukiyar mutane, hakazalika ya gargadeni kada inyi ta'amuni da kwaya da kuma neman mata. Shi yasa ba na daukan abinda ba nawa ba.

Saboda haka nike cike masa alkawari na.

DT: Shin tun lokacin da ka mayar da kudin, me ka fuskanta daga yan uwanka da abokai?

Kofura Umar: "Wasu suna zagi na. Wasu sun ce ba zan taba arziki ba a rayuwata. Amma kuma wasu sun yaba min; na ji maganganu daban-daban. Amma ba na nadamar abinda nayi. Bai ina farin cikin mayar da kudin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel