Kasar Laberiya ta karrama shugaba Muhammadu Buhari (Hotuna)
A ranar Juma'a, gwamnatin kasar Laberiya ta karrama shugaba Muhammadu Buhari da lambar yabo mafi girma da karamci na kasar.
Kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu, a jawabin da ya saki ya ce an baiwa shugaba Buhari lambar yabon ne a bikin murnar shekaru 172 da samun yancin kan kasar Laberiya a Monrovia, babbar birnin Laberiya.
Buhari ya sadaukar da wannan lambar yabo ga yan Najeriya da dukkan sojin Najeriyan da suka rasa rayukansu a yakin taimakawa Laberiya.
Garba Shehu ya ce shugaban kasan ya godewa mutanen Laberiya da wannan lambar yabo kuma ya jaddada niyyar karfafa alaka da kasar.
A jawabin da Buhari yayi, ya yiwa kasar Laberiya alkawarin turo yan Najeriya 50 domin taimakawa wajen gina kasar.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
KU KARANTA: Da duminsa: Kotu ta alanta Shi'a matsayin haramtacciyar kungiya

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng