Hali abokin tafiya: An karawa salihin soja, Bashir Umar, girma

Hali abokin tafiya: An karawa salihin soja, Bashir Umar, girma

Babban hafsan sojin saman Najeriya a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja ya karawa jami'in sojan sama, Bashir Umar, wanda ya mayar da kudi Yuro 37,000, kimanin milyan 15, da ya tsinta a kasuwar masaukin manniyyata aikin Hajji a Kano.

Air Marshal Sadique Abubakar, ya kara masa girma zuwa matsayin Kofura daga ACM. Ya bayyana cewa wannan zai zama darasi ga sauran jami'an hukumar da kuma nuna cewa hukumar sojin sama na masu gaskiya, aminci da mutunci ne.

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon fatan alheri da yabo ga salihin jami'in hukumar sojin saman Najeriya, ACM Bashir Umar, wanda ya dawo da makudan kudin da ya tsinta mallakin wani.

ACM Bashir Umar, wanda ya kasance dan agajin kungiyar Izalah kafin ya zama jami'in soja ya dawo da kudi Yuro 37,000, kimanin milyan 15 ga wani Alhaji Ahmed, wanda ya yarda kudin a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, 2019 a kasuwan sansanin maniyyata aikin Hajji dake jihar Kano.

A cewar Buhari, "Gaskiya da Amana zasu cigaba da kasancewa halayen kwarai, duk da kalubalen da ake fuskanta a kasa."

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An tantance ministoci 24, saura 16 (Jerin sunayen)

Hali abokin tafiya: An karawa salihin soja, Bashir Umar, girma
Hali abokin tafiya: An karawa salihin soja, Bashir Umar, girma
Asali: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel