Ku gaggauta barin yankin mu ko mu yi 'fito na fito' da ku - Afenifere ta gargadi makiyaya

Ku gaggauta barin yankin mu ko mu yi 'fito na fito' da ku - Afenifere ta gargadi makiyaya

Afenifer, babbar kungiyar 'yan kabilar Yoruba, ta umarci Fulani Makiyaya da ke yankin kudu maso yamma da su gaggauta barin yankinsu ko kuma su fuskanci fushinsu, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito ranar Alhamis.

Yayin wani taro da manema labarai da shugabannin kungiyar suka yi a Legas, Afenifere ta roki majalisun kasa da kar su canja dokar da zata bawa gwamnatin tarayya ikon karbar filaye daga gwamnatin jihohi domin yin tsarin Ruga.

Da yake karanta jawabi amadadin sauran shugabannin kungiyar, Dattijo Ayo Adebanjo, ya ce ba zasu yarda kashe-kashen da ake yi a yankin ya cigaba ba.

Ragowar shugabannin kungiyar da suka halarci taron sun hada da Banji Akintoye, Femi Okunrounmu, Yinka Odumakin, Supo Shonibare da Sola Lawal.

Adebanjo ya ce kungiyar Afenifere na bukatar Fulani makiyaya su gaggauta barin yankin kudu maso yamma ko kuma idan sun ki, jama'ar yamkin su yi 'fito na fito' da su.

DUBA WANNAN: An tsinci gawar soja da wani rubutu a takarda a barikin sojoji a Abuja

Wani bangaren na jawabin kungiyar ya ce, "ba zamu yarda mutanen da suka ki yarda zababbun gwamnonin mu su kafa 'yan sandan jihohi ba yanzu kuma suke son karbar kasar mu domin yi wa makiyayan da suka hana mu zama lafiya wurin zama ba.

"Mu na bukatar su gaggauta barin kasar 'yan kabilar Yoruba. Kuma idan suka ki yin hakan nan da dan wani lokaci, ba zamu hana mutanen mu yin 'fito na fito' da su ba."

Kungiyar ta kara da cewa ba zata yarda ta zuba ido ba a yayin da ake cigaba da zubar da jinin 'ya'yanta ba don kawai ana ikirarin zama a kasa daya mai bin tsarin tarayya ba. Kazalika, sun yi kira da a gaggauta koma wa tsarin mulki da ya bawa kowanne yanki damar cin gashin kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel