Babban Magana: Makafi sun yi korafi kan hana su minista a gwamnatin Buhari

Babban Magana: Makafi sun yi korafi kan hana su minista a gwamnatin Buhari

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar makafi ta arewa ta yi korafi akan rashin ba su mukamin minista a gwamnatin jam’iyyar Allah Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sakataren kungiyar, Muntari Saleh dai yayi Allah wadai da jerin sunayen ministocin da Shugaban kasar ya aika majalisar dattawa domin tantancewa.

A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saki jerin sunaye 43 na ministocin Najeriya.

Muntari Saleh ya ce ya kamata mutane masu nakasa su samu wakilci a jerin ministocin.

Ya kara da cewa nakasa ba kasawa ba ce, tun da ba ido ko hannu ne ke rike minista ba, ilimi ne.

“Mun ga an ba da sunayenn ministoci guda 43, amma mun duba mun kasa kunne ba mu ji sunan namu ko mutum daya ba.

“Ba mu ji sunan makaho ko gurgu ko kurma ko kuturu ba, wanda aka ce shi ma an ba shi minista yau, domin mu tabbatar ana yi damu.

KU KARANTA KUMA: Tantance ministoci: An samu sabani tsakanin Sanatocin APC da na PDP kan rabon aiki

"Amma abunda zai baka mamaki, idan neman kuri'a ne sai a neme mu, sai a bimu lungu-lungu, kauye-kauye, a sanyamu mu hada jama’armu a sanya mu yin taro. Kamar yadda kowa ke bad a kuri’u muma haka muke ba da tamu, kamata yayi idan aka yi tuwo da garinka toh kada a hana ka.

“Yau idan aka bamu ministanmu anan ne za a rage masu yawan barace-barace, sai ta kai an nemi mai bara ko daya ba a samu ba,” inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel